UBA YI MAGANA DA NI
1. Uba yi magana da ni
Domin in yi da mutane
Yadda ka nemi tumaki
Bari in nemi mutane
Yi amfani da ni Allah
Kullayaumi a ko’ina
2. Ka bi da ni Ubangiji
Domin in bi da batattu
Ciyar da ni domin in ba
Abinci ga mayunwata
3. Karfaffa ni domin in tsaya
A kan Yesu dutsen ceto
In mika hannu ga masu
Fada da tekun duniya
4. Koya mani Ubangiji
Asirai na samaniya
Ka iza magana na yau
Zuwa zuciyar masu ji
5. Ka ba ni hutun nan naka
Ka cika ni da ikonka
In yi maganar alheri
Ga masu bacin zuciya
6. Ka cika ni Ubangiji
Cika zuciyata sosai
Da wutarka na falkawa
In yi kauna da yabonka
7. Yi amfani da ni Uba
Kullayaumi a ko’ina
Har in ga fuskarka a can
Hutu da daukaka nawa
----------------------------------------------------------------------------------------------
1. Lord speak to me that I may speak
In living echoes of Thy tone;
As Thou hast sought, so let me seek
Thy erring children, lost and lone.
O use me Lord use even me
Just as Thou wilt and when and where
2. Oh, lead me, Lord that I may lead
The wandering and the wavering feet;
Oh feed me, Lord that I may feed
Thy hungering ones with manna sweet.
3. Oh, strengthen me, that while I stand
Firm on the rock and strong in Thee
I may stretch out a loving hand
To wrestlers with the troubled sea!
4. Oh, teach me Lord that I may teach
The precious things Thou dost impart;
And wing my words that they may reach
The hidden depths of many a heart!
5. Oh, give Thine own sweet rest to me,
That I may speak with soothing power,
A word in season, as from Thee,
To weary ones in needful hour.
6. Oh, fill me with Thy fullness, Lord,
Until my very heart o’erflow
In kindling thought and glowing word,
Thy love to tell, Thy praise to show.
7. Oh, use me Lord, use even me,
Just as Thou wilt, and when, and where,
Until Thy blessed face I see,
Thy rest, Thy joy, Thy glory share.
CLICK HERE TO LISTEN TO TUNE
Comments
Post a Comment