ALMASIHU HASKEN DUNIYA
1. Almasihu, hasken duniya Begen dukan masu rai, Yesu Rasul, Kalmar Allah Tun fil azal kai kadai Kai kadai madawwami ne Kai kadai madaukaki 2. Kai ka ajiye rigar mulki Ka bar duk don cetonmu Zafin mutuwa ba ka ki ba Duk ka sha don kaunarmu Karbi yabo, karbi mulki Naka ne har abada 3. Mutuwa ta rasa iko Bisanka Mai Nasara Lahira ta bude kofa Ka shiga, har ka fita An dauke ka can a sama Aikinka ka gama nan 4. Duk jama’a suna jiran Zuwanka, ya Almasihu Duk Ekklesiya tana zaman Kewarka Mai Cetonta Zo da sauri, muna bege Zo mu dinga ganinka 5. Al’ummai ku kasa kunne Shi ne Ubangijinku Ruhun Allah kai mutane Zuwa gun Mai Cetonsu Dan Maryamu, Tsatson Dawuda Ibnu Llahi, Dan Mutum (Littafin Waqoqi 89) ---------------------------------------------------------------------------------------------- 1. Jesus Christ the light of this world Hope of every living being You the Spirit and Word of God Thou art from everlasting You alone...
Comments
Post a Comment