A CAN CIKIN BIRMIN DAUDA


1. A can cikin birnin Dauda
Ga wurin kiwon garke
Inda jariri ya kwanta
Komi ne shimfidarsa
Maryarmu ce uwarsa
Yesu Kristi ne danta

2. Ya zo daga samaniya
Shi Allah, Ubangiji
Masaukinsa a riga ne
Cikin komin tumaki
Da talakawar duniya
Yesu ya ci ya sha kuwa

3. Ya yi girman ban mamaki
Ya nuna ladabi kuwa
Yana kaunar uwatasa
Da ta rene shi sosai
Yakamata ya’yan krista
Su yi koyin halinsa.

4. Mun sami fasali mai kyau
Cikinsa kullayaumi
Shi rarrauna marar karfi
Mai kuka da hawaye
Ya san dukan kasawarmu
Da farincikinmu ma

5. Daga karshe za mu gan shi
Ta wurin fansar kauna
Wannan yaro mai ladabi
Shi ne Ubangijinmu
Zai kai mu can mulkinsa
In da shi kansa yake

6. Ba a komin tumaki ba
A tsakanin dabobbi
Za mu gan shi amma sama
Hannun dama na Allah
Zai ba mu rawanin rai
A gaban kursiyinsa.


----------------------------------------------------------------------------------------------


1. Once, in royal David’s city,
Stood a lowly cattle-shed,
Where a mother laid her Baby,
In a manger for His bed.
Mary was that mother mild,
Jesus Christ her little Child.

2. He came down to earth from heaven,
Who is God and Lord of all,
And His shelter was a stable,
And His cradle was a stall:
With the poor and mean and lowly
Lived on earth our Saviour holy.

3. And through all His wondrous childhood
He would honour and obey,
Love and watch the lowly mother,
In whose gentle arms He lay.
Christian children all must be
Mild, obedient, good as He.

4. For He is our childhood’s pattern,
Day by day like us He grew;
He was little, weak and helpless;
Tears and smiles like us He knew:
And He feeleth for our sadness,
And He shareth in our gladness.

5. And our eyes at last shall see Him,
Through His own redeeming love;
For that Child, so dear and gentle,
Is our Lord in heaven above;
And He leads His children on
To the place where He is gone.

6. Not in that poor, lowly stable,
With the oxen standing by,
We shall see Him; but in heaven,
Set at God’s right hand on high;
When like stars His children crowned,
All in white shall wait around.

CLICK HERE TO LISTEN TO TUNE

Comments

Popular posts from this blog

ALMASIHU HASKEN DUNIYA

DOGARA GA SUNAN YESU

GA BABBANNN LIKITARMU NAN (61)